Yanzu-Yanzu: An bindige jami'in DSS har lahira a Imo


An yi wa jami'in hukumar yan sandan farin kaya DSS, kisar gilla a garin Owerri, babban birnin jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na faruwa ne kasa da awa 48 bayan kona ofishin hukumar da aka yi a Nnewi, jihar Anambra.

Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo

Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo Source: Original

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa an bindige jami'in mai suna Prince Nwachinaemere Ezemuonye Ozuzu, daga Umuoyo, Irete, karamar hukumar Owerri West a hanyar Owerri/Onitsha.

An ce an tura jami'in ya yi wani aiki ne a Anambra awanni kadan bayan kona ofishin DSS na Nnewi.

An kashe shi ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta komawa wurin aikinsa.

A halin yanzu babu cikakken bayanin kan yadda ya mutu duba da cewa wani rahoton ya ce ya mutu ne sakamakon kuskuren harbi.

An ce wani abokin aikinsa ne ya harba bindiga bisa kuskure kuma harsashin ya same shi.

Daya daga cikin yan uwansa, Deacon Daniel Opara, wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

Ya ce:

"Ba mu samu cikaken bayani kan ainihin abin da ya faru ba domin an yi ikirarin cewa wani dan sanda da suke aikin hadin gwiwa tare ne ya bindige shi bisa kuskure a wurin aiki a jihar Anambra.

"Iyalansa na zargin akwai lauke cikin nadi duba da cewa a baya-bayan nan aka yi masa karin girma.

"Ya fara aiki da DSS kimanin shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata kuma yana da aure da 'ya'ya hudu."

Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, CSP Mike Abattam ba domin wayansa ya yi ta ringing amma bai daga ba.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN