Yan sandan Kano sun kama mutum bakwai da zargin kashe fasto


Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 7 da take zargin da kisan wani fasto kuma shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya mai suna CAN.

'Yan sandan sun ce kisan shugaban mai suna Shu’aibu Yahona ya biyo bayan wata hatsaniya da ta ɓarke tsakanin wani matashi da matar yayansa, inda ya buga mata taɓarya a ka, abin da kuma ya yi sandiyar mutuwarta nan take.

Da yake yi wa BBC karin bayani, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna kiyawa ya ce an kashe Fasto Shu'aibu ne a garin Masu da ke yankin Ƙarmar Hukumar Sumaila saboda an zarge shi da bai wa matashin da ake zargi da kashe matar yayan nasa.

Wakilin BBC a Kano Khalifa Dokaji ya ruwaito cewa matashin ya miƙa kansa ga 'yan sanda bayan ya je gidan Shu'aibu, wanda hakan ya tilasta wa faston barin gari.

Sai dai daga bisani ya koma garin inda kuma matasa suka far masa.

Rabaran Samuel Adeyemo, shi ne shugaban ƙungiyar CAN ta Najeriya a Kano kuma ya nemi gwamnatin jihar da ta biya su diyya tare da neman a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kisan malamin.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN