Yanzu haka ana sheka ruwan sama har da kankara a garin Birnin kebbi na jihar Kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa
Hadari ya hadu cikin yan mintuna, kuma ya gwabce da ruwan sama da karfe 5 na yammacin ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba 2021.
Wannan yana faruwa ne bayan jinkirin ruwan sama na wani dan lokaci a garin Birnin kebbi
Yanzu haka a Unguwar Bayan Kara a garin Birnin kebbi, ana ruwan sama har da kankara, lamari da aka dade ba a sami irinsa ba daga farkon damanan bana.