Type Here to Get Search Results !

Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi a Rivers


Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta samo gawar basarake mai shekaru sittin da daya wanda aka sace a shekarar 2019. 

Jami'an 'yan sanda sun samo gawar Chief Robert Loolo ne a wasu yankuna da suka hada garuruwan Luwa, Bera da Bane, Daily Trust ta ruwaito. 

Dan mamacin mai suna Dr Douglas Fabeke, ya sanar da manema labarai cewa, sau biyu suna biyan kudin fansa domin samun kubutar da mahaifinsa daga hannun miyagun.

Ya ce an azabtar da basaraken kuma an daure shi a wani itace inda aka bar shi ya mutu kafin ya samu daukin jama'a.

"Wata kungiyar matasa ta je har gida, suka yi awon gaba da shi kan rikicin da suke yi na shugaban matasa. Mun yi kokarin rokon matasan su sako su, mun biya kudin fansa har sau biyu.

"Mun kai wa 'yan sanda da dukkan jami'an tsaron jihar korafi, sun shiga kuma sun yi kokarin ganin an sako shi amma shiru," dan shi ya tabbatar.

"Mun cigaba da bincike a watanni kadan da suka gabata, mun kama wani mai maganin gargajiya wanda ya ce an kashe shi sai dai bai san inda aka birne shi ba..

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies