Yadda ƴan bindiga suka tarwatsa garuruwa 10 a Zamfara


Hare-haren 'yan fashin daji sun tarwatsa al'ummomin wasu garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, bayan halaka wasu mutane da sace dabbobi da kuma ƙoƙƙona shaguna da dai sauransu da 'yan fashin suka yi.

Yanzu haka dai jama'ar garuruwan da abin ya shafa suna can suna zaman gudun hijira a wasu ƙananan hukumomi da ke makwaftaka da karamar hukumar ta Zurmi.

Bayanai sun ce yanzu haka jama'ar garin Ƴan Ɓuki da yankunan karamar hukumar da dama sun shiga halin ƙaƙanikayi tun bayan da 'yan bindigar suka tsaurara hare-haren da suke kai musu a ranar Lahadin da ta gabata.

Wani mazaunin garin ƴan Ɓuki da ya buƙaci mu sakaye sunansa, ya shaida wa BBC cewa garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗar da Ƴan Ɓuki, da Ditsi, da Kada Musa, da Gidan zago, da Marmaro, da Dada, da Maduba, da Kwata, da Oho, da Fushin Buku da Gandasau.

''Dukkan wadannan garuruwa ina tabatar muku da cewa yanzu babu kowa a cikinsu, a halin da muke ciki, sun yi gudun hijira, yanzu idan ka je garin Ƙauran Namoda za ka tabbatar da su ne suka taru a can, sannan wasu suna Gusau babban birnin jiha''.

Shaidar ya kara da cewa a halin da ake ciki duk wanda 'yan bindigar suka gani a waɗannan garuruwa suna kashe shi ne ko kuma su kama su tafi da shi daji, ''suna zazzagayawa, har suna barazanar cewa duk wanda ya je shiga gona don dibar gyada ko dawarsa, to ya sani za su kashe shi''

A cewarsa ''Yanzu haka akwai mutane 45 wadanda suka dauki mutanen garin Dutsi, wadanda suke can a hannunsu, babu matakan da tsaron da aka dauka har zuwa wannan lokaci.

Shi ma wani mutumin garin na Yan Ɓuki da ya tsallake rijiya da baya ya shaida wa BBC Hausa cewa sun shiga garin ne da yawa a kan babura suna buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

''Suna bi gida-gida suna fasa dakuna suna shiga, kuma da sun ga mutum ba abin da suke yi illa su harbe shi su yi gaba, su je su kwashi dabbobi su ara gaba, sun tafi da awaki sun fi ɗari biyar, saniya kawai, don tinkiya ta fi dubu wadda suka tafi da ita'' inji wannan shaida.

Ya kara da cewa washe garin ranar da aka kai harin sai da suka binne mutane bakwai da suka gamu da ajalinsu yayin wannan farmaki da 'yan bindigar suka kai.

To sai dai a tattaunawarsa da BBC, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce sun samu labarin abin da yake faruwa a yankin na Zurmi, har ma an aika da jami'an 'yan sanda kusan mota bakwai domin tunkarar 'yan bindigar.

''Sun je sun yi rangadi, domin tabbatar da abubuwan da ke faruwa da kuma karawa mutane kwarin guiwar cewa jami'an tsaro na sane da abubuwan da ke faruwa, kuma a shirye take ta kare rayukansu da dukiyoyoinsu, inji kakakkin 'yan sandan.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN