Wata huɗu babu labarin ɗaliban Yawuri


Yanzu haka iyayen daliban sakandiren tarayya ta Yawuri a jihar Kebbi da 'yan bindiga suka sace na ci gaba da bayyana damuwa kan tsawon lokacin da 'yayan nasu suka shafe a daji.

Ɗaliban dai yanzu haka sun shafe kimanin wata hudu bayan sace su, abin da ya sa iyayen yaran ke cewa sun yanke ƙauna da alwashin ceto 'yayan nasu da gwamnatin jihar Kebbi ta daɗe tana yi.

Wani mahaifi da ke cikin wadanda suka rasa 'ya'yansu, ya shaida wa BBC cewa yanzu haka suna cikin matukar tashin hankali sakamakon rashin sanin halin da 'ya'yan na su ke ciki,

A cewarsa ''Daga cikinmu ma wasu sun rasu, wasu sun hadu da rashin lafiya, mu kanmu wallahi tallahi da za a je a gwada mu sai an ga hawan jini ya kama mu, saboda halin da muke ciki na tashin lankali.''

Ya kara da cewa ''Matan mu ne ma abin ya fi tayar musu da hankali, wani abin idan muna gaya muku sai ku ji kamar ma ba gaskiya muke fadi ba, kullum a ce yau a ce gobe, amma babu wani abu da muka gani a kasa har zuwa wannan lokaci''.

Shi ma wani daga cikin wadanda 'ya'yansu ke hannun 'yan bindigar ya bukaci gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa domin ganin an kubutar da yaran cikin koshin lafiya.

Shi dai gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu, ya lashi takobin kwato yaran tun lokacin da aka sace su, sai dai har zuwa wannan lokaci babu labarnsu, ko ma na irin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na kubutar da su.

Yayin wani taro bayan sace daliban, gwamnan ya ce ''za mu shiga daji mu kwato su, dama abun da aka rantsar da mu mu yi kenan, don haka duk wanda ke ganin zai dauki yaranmu muna da rai ya yi karya''

Sashen Hausa na BBC ya shafe kusan sa'oi 7 yana kokarin ji daga bakin mahukuntar jihar ta Kebbi game da alkawarin da gwamnan ya yi na ceto yaran, amma hakanmu bai cimma ruwa ba har zuwa lokacin rubuta wannan labari.

Ranar 16 ga watan Yunin shekarar nan ta 2021 ne dai 'yan bindigar suka sace wadannan dalibai daga makarantarsu, inda suka kwashe su, su sama da 100 da wasu malamansu, suka tafi da su daji.

Satar mutane don neman kudin fansa musamman dalibai, matsala ce da ta zama ruwan dare a fadin Najeriya a shekarun baya-bayan nan, sai dai mahukunta na cewa suna yin iya bakin kokarinsu don shawo kan matsalar, amma kuma kusan matsalar sai karuwa take yi.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN