Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Litinin 11 ga watan Oktoba, ya ba da sanarwar cewa nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara kera makamai yayin da kasar ke fama da kalubalen tsaro ta fuskoki da dama.
Ya ce an umarci Ma’aikatar Tsaro da ta samar da katafaren rukunin masana’antun soji don fara kera makamai na cikin gida saboda biyan bukatun sojojin kasar a yaki da suke da tashe-tashen hankula, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin bude wani taron bita na kwanaki biyu na ayyukan ministoci wanda aka shirya don tantance ci gaban da aka samu don cimma muhimman abubuwa tara na wannan Gwamnatin.
Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
.Shugaban ya ce kafa katafaren masana’antar soji zai magance dogaro da Najeriya ke yi kan wasu kasashen wajen samar da kayan aikin soji.
Ya ce ana aiwatar da aikin ne a karkashin DICON, wani sashin soja da ke da alhakin kera makamai.
A sauran kokarin karfafa tsaron kasa, Shugaban ya ce abin farin ciki ne ganin Najeriya ta karbi jiragen A-29 Super Tucano.
Ya ce ana amfani da jiragen ne don horarwa, sa ido da kai hari.
Najeriya na fuskantar rashin tsaro ta fuskoki da dama yayin da sojoji ke fafatawa da 'yan ta'adda a arewa maso gabas da ma sauran sassan kasar.
Jihohi a Arewa maso yamma sun fara daukar matakai kan kalubalen tsaro, ciki har da katse hanyoyin sadarwa, kamar a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.
Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aikin tukuru
A wani labari, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya karanto dokar tarzoma ga ministoci a majalisar ministocinsa da sakatarorin dindindin a fadin ma'aikatu.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shugaban ya bukaci jami'an da su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci.
Shugaban ya ce yana da mahimmanci jami'an su sani cewa sauke nauyin ayyukansu da muhimmanci zai taimaka wa gwamnatin yanzu ta cimma burin ta da alkawuran da ta yiwa 'yan Najeriya.
Legit Hausa