Rikicin Shugabancin APC a Kano: Shekarau ya bayyana matakin da ya ɗaukaTsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahin Shekarau, ya bayyana cewa yana nan daram a cikin jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan, wanda a halin yanzun yake wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, yace ba gudu ba ja da baya kan sabon shugaban APC na Kano, Ahmadu Haruna Danzago.

Sanata Shekarau ya faɗi haka ne a wani rubutu da ya buga a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Shekarau yace:

"Ina son amfani da wannan damar wajen sanar da abokai da yan uwa halin da jam'iyyar APC take ciki a jihar Kano."

"Ni, Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci mambobin majalisar tarayya mun kai ƙorafi sakateriyar APC ta ƙasa kan yadda ake tafiyar da jam'iyya ba tare da mu ba."

"Zaɓar mu aka yi, kuma mutane suna da damar sanin abubuwan dake tafiya a cikin jam'iyya, an karbi korafinmu da mutuntawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana."

Waye shugaban APC reshen Kano?

Sanata Shekarau ya ƙara da cewa babu wanda ya sani a matsayin shugaban APC reshen jihar Kano sai Ahmadu Haruna Danzago.

"A jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam'iyyar APC zababbe a gurinmu. Muna yi masa addu'ar Allah ya karfafi zuciyarsa kuma Allah ya taya shi riko."

Ina nan daram a cikin APC - Shekarau

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa yana nan daram a cikin jam'iyyar APC kuma ba ya fatan fita amma ba zai yarda da wulaƙanci da sakarci ba.

"Ina mai sanar da duk jama'armu cewa, ina cikin jam'iyyar APC daram-dam, zamu tsaya har inda Allah ya so."

"A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba zamu lamunci sakarci ba."

Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba zamu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka."

A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya.

Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN