Da duminsa: Yan bindiga sun sace yar NYSC kan hanyarta ta zuwa jihar Kebbi domin yi wa kasa hidima


Yan bindigan da ake zargin yan fashin daji ne sun sace wata budurwa mai suna Iorliam Jennifer Awashima kan hanyarta na zuwa jihar Kebbi domin yi wa kasa hidima. 

Bayanai sun nuna cewa ta kammala karatun ta na Digiri a fannin yaren Turanci a Jami'ar jihar Benue. Sakamakon haka aka turo ta jihar Kebbi domin yi wa kasa hidima a rukunin na 2021 Batch C Stream One orientation course,

Rahotun LIB ya ce lamarin ya faru ne a yankin jihar Zamfara ranar Laraba 20 ga watan Oktoba.

Kazalika rahotun ya ce ce yan bindigan sun sace ta ne tare da sauran fasinjojin da suke cikin mota tare. Sai dai direban motar tare da wasu fasinjoji sun sami tserewa daga hannun yan bindigan. 

Bayan tabbatar da faruwar lamarin, mai karadun kare hakkin bil'adama na jihar Benue Ukan Kurugh ya roki duk wanda ke da wani bayani kan lamarin ya kira lambar waya: 07032164404 ko ya kai bayani a ofishin yansanda mafi kusa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN