Sakamakon toshe layukan sadarwa a wasu jihohin Arewa maso yamma, yan bindiga sun kasa tuntubar iyalan wadanda suka sace ta waya, yanzu sun koma rubuta wasika.
Wannan sabon salo ya bayyana ne a jihar Sokoto inda yan bindiga suka aikawa Dagacin Burkusuuma a karamar hukumar Sabon Birni. A cikin wasikar, yan bindigan sun bukaci Dagacin ya nemi kudi daga wajen iyalan wadanda suka sace da abokansu na arziki.
A wasikar dake dauke sunayen mutum 19, yan bindigan sun bukaci daya daga cikin wadanda suka sace ya bayyana halin da suka ciki. Sokoto.
A wasikar da Legit ta gani, an bayyana sunayen wadanda aka sace da kuma kudi N20m da ake bukatar kudin fansa.
Ga jerin sunayensu:
Maza
1. Yahaya
2. Bello Sani
3. Maharazu Mamman
4. Naziru Saidu
5. Lawali Nano
6. Abdullahi M Makau
7. Ashe Sani Mamman
8. Mustafa Abdullahi
9. Hussaini Ladan Samaila
Mata
1. Rashida Abdullahi
2. Rahila Abdullahi
3. Hana M isah
4. Hauwa
5. Maryam Sani
6. Hadiza Labaran
7. Jimma Maidabo Gatawa
Yara
1. Safiya A Sani
2. Aisha Labaran
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka