Tsawon shekaru, an kashe 'yan Najeriya da yawa yayin da hukumomin tsaro ba su gano wadanda suka kashe su ba.
A cikin wannan kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito, Legit.ng ta lissafa wasu daga cikin wadannan shari'o'in kisan kai da kisan gilla wadanda har yanzu ba a bayyana makasan ba.
1. Bola Ige
An haifi Ige ranar 13 Satumba 1930 a Osun kuma aka kashe shi a ranar 23 ga Disamba, 2001 a Ibadan.
2. Dele Giwa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An haife shi a ranar 16 ga Maris 1947 kuma an kashe shi ranar 19 ga Oktoba, 1986
3. Kudirat Abiola
An haife ta a 1951 kuma an kashe ta ranar 4 ga Yuni, 1996
4. Funsho Williams
An haife shi a ranar 9 ga Mayu, 1948 kuma an kashe shi ranar 27 ga Yuli, 2006
5. Eunice Olawale
An haife ta a ranar 23 ga Yuli, 1974 kuma an kashe ta a ranar 9 ga Yuli, 2016
6. Marshal Alex Badeh (mai ritaya)
An harbe Badeh a kan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi a ranar 18 ga Disamba, 2018, yayin da yake dawowa daga gonarsa.
7. Chief Alfred Rewane
An kashe shi a ranar 6 ga Oktoba, 1995, tsakanin 8:15 na safe zuwa 8:30 na safe a gidansa da ke Ikeja, jihar Legas, wasu mutane biyar da har yanzu ba a san su ba suka kashe shi.
8. Marshall Harry
An yi masa kisan gilla a gidansa da ke Abuja kafin zaben shugaban kasa na 2003.
9. Dipo Dina
An kashe shi a ranar 25 ga Janairu, 2010.
10. Brig. Janar Lasun Odeleke
A 1990, Odeleke ya mutu a asirce a Abuja. A cewar wani rahoto na hukuma, direban da ya buge shi ya kashe shi ya gudu, amma ba a ba dangin damar gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsa ba.
11. James Kalto
A ranar 12 ga Nuwamba, 1995, aka sace tare da kashe James Kalto, dan jarida kuma tsohon marubuci tare da Tell da Tempo.
12. Chief Aminasoari Dikibo
An kashe shi a ranar 6 ga Fabrairu, 2004.
13. Barnabas Igwe
A shekarar 2002, an kashe Barnabas Igwe, shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (reshen Onitsha), da matarsa, Abigail.
14. Olaitan Oyerinde
A ranar 4 ga Mayu, 2012, an kashe Kwamared Olaitan Oyerinde, Babban Sakataren Gwamnati (PPS) na Gwamnan Jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole.
15. Mista Godwin Agbroko
16. Abayomi Ogundeji
17. Bayo Oh
Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu
A wani labarin, Duk da cewa har yanzu ba a kawo karshen yaki da ta'addanci ba a Nigeria, an samu wasu cigaba a shekarar 2021.
Kawo yanzu, an kashe a kalla shugabannin yan bindiga da yan ta'adda 12 a yayin da hukumomin tsaro ke cigaba da yaki da bata garin da ke adabar kasar.
Ga dai jerin sunayen shugabannin yan ta'addan da aka kashe a shekarar 2021 bisa sanarwar da rundunar sojojin Nigeria da rahotonni da sauran kafafen watsa labarai ke fitarwa.
Source: Legit.ng
Rubuta ra ayin ka