Jerin sunayen kwamandodin boko haram da yan bindiga da soji suka kashe a 2021


Duk da cewa har yanzu ba a kawo karshen yaki da ta'addanci ba a Nigeria, an samu wasu cigaba a shekarar 2021.

Kawo yanzu, an kashe a kalla shugabannin yan bindiga da yan ta'adda 12 a yayin da hukumomin tsaro ke cigaba da yaki da bata garin da ke adabar kasar.

Ga dai jerin sunayen shugabannin yan ta'addan da aka kashe a shekarar 2021 bisa sanarwar da rundunar sojojin Nigeria da rahotonni da sauran kafafen watsa labarai ke fitarwa.

1. Abubakar Shekau

Bayan shekaru da dama ana ayyana cewa ya mutu amma ya sake bulowa, daga karshe an ruwaito cewa an kashe Abubakar Shekau, shugban kungiyar Boko Haram a watan Mayu.

A cewar The Cable, dan sanda mai binciken sirri ya ambato cewa kwamandojin kungiyar ISWAP, kungiyar ta da balle daga Boko Haram, na cewa Shekau ya kashe kansa da bam "lokacin da ya lura mayakan ISWAP ne son kama shi da ransa."

2. Abu Mus'ab Albarnawi

A ranar A;hamis, 14 ga watan Oktoba, babban hafsan tsaro na kasa, CDS, Janar Lucky Irabor ya tabbatar da kashe shugaban ISWAP, Abu Mus'ab Albarnawi.

Al-Barnawi dan wanda ya kafa Boko Haram ne, Muhammad Yusuf wanda shima yan sanda sun kashe shi a 2009 a farkon lokacin da kungiyar ke kafuwa.

3. Yaya Ebraheem

PR Nigeria ta ruwaito cewa Yaya Ebraheem na daya daga cikin kwamandojin ISWAP da ya yi yunkurin kai wa tawagar sojoji hari na ranar Laraba 13 ga watan Oktoba a Ngamdu a Borno. Amma, shima an ruwaito cewa sojoji sun kashe shi.

4. Baba Chattimari

Baba Chattimari, kwamandan ISWAP, shima an ruwaito cewa an kashe shi tare da Ebraheem.

5. Abu Adam Oubaida

Abu Adam Oubaida shine kwamandan ISWAP na uku da aka ruwaito cewa sojoji sun kashe a yankin Ngamdu.

6. Auwalun Daudawa

Auwalun Daudawa hatsabibin dan bindiga ne wanda ya jagoranci sace dalibai 300 na makarantar sakandare ta Kankara a jihar Katsina a Disamban 2020.

A watan Fabrairun 2021, Daudawa ya ajiye makamansa ya rungumi shirin sulhu na Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.

Amma, kwanaki kadan bayan mika wuyarsa ya koma daji ya cigaba da laifukansa da ya saba.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Zamfara, Abubakar Dauran ya ce Daurawa ya shaidawa wasu mutane cewa zai tafi daurin auren wasu yan uwansa ne.

Sai dai, ya sashe shanu fiye da 100 ya kashe mai kiwonsu, a cewar kwamishinan. Wasu mutane a yankin sun mayar da martani sun halaka shi kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Amma a rahoton da Daily Trust ta wallafa, an kashe Daudawa ne yayin musayar wuta da wata kungiyar yan bindigan masu gaba da shi a tsakanin karamar hukumar Zurmi a Katsina da Batsari a Katsina.

7. Jauro Daji

Jauro Daji shima wani hatsabibin dan bindiga ne da ya dade yana adabar mutanen jihar Niger.

Yan sanda, tare da taimakon yan banga sun kashe Daji da wasu yan bindigan da dama masu masa biyaya a yankin Kontagora na jihar a ranar Litinin 30 ga watan Agusta.

8. Habu Nabayye

9. Isuhu Sadi

10. Murtala Danmaje

Nabayye, Sadi da Danmaje shugabannin yan bindiga ne a jihar Zamfara. A cewar PR Nigeria, sojojin saman Nigeria ne suka kashe su yayin ruwan wuta da suka yi a dajin Kuyanbana.

11. Alhaji Karki Buzu

12. Yalo Nagoshi

PR Nigeria ta rahoto cewa an kashe Buzu da Nagoshi a watan Oktoba a jihar Niger. An ce suna cikin yan bindiga 32 da suka tsere daga Zamfara kafin dakarun sojojin Nigeria suka katse musu hanzari.

Source: Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN