Jami’an DSS sun kama Hadimin Gwamna, mutum 2 da zargin satar kudin da aka ware wa talakawa


Jami’an tsaro masu fararen kaya na DSS sun aika sammaci ga wani hadimin gwamnan jihar Bayelsa, Morris Asaunuku bisa zargin wawurar kudi.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, 2021, jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa ana zargin Hon. Morris Asaunuku da wasu mutane biyu da laifin sata.

Zargin da hukumar DSS take yi wa wadannan mutane shi ne sun yi karya, sannan sun dauke Naira miliyan 4.6 da aka ware domin al’ummar kauyen Adiegbe.

Rahoton yace kamfanin man Nigerian Agip Oil Company watau NAOC, shi ne ya bada wannan kudi domin mutanen Adiegbe da ke karamar hukumar Ekeremor.

A kokarin binciken wadanda suka taba wannan kudi ne DSS ta aika wa Asaunuku wanda shi ne mai ba gwamnan Bayelsa shawara a kan shari’a, goron gayyata.

A dalilin wawurar wadannan miliyoyin kudi ne rikici ya barke a yankin Ekeremor, jihar Bayelsa.

Wata majiya a kauyen Adiegbe ta shaida cewa ana zargin wadannan mutane uku da yin karya da sunan Mai martaba Sarki, Benedict Thompson, wajen cin kudin.

Sauran wadanda ake zargi da laifi

Wadannan mutane da ke hannun DSS da kuma wani Godbless Berekpebede wanda ya fake da sunan shugaban matasan yankin, sun yi awon gaba da miliyoyin.

Daga cikin wadanda aka ambata a badakalar har da wata mata, Rose Asanaku. Rahoton yace Asanaku tayi karyar tana cikin jagororin matan kauyen Adiegbe.

Mutanen wannan kauye ne suka kai korafin su Asaunuku wajen mataimakin gwamnan Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo da DSS, ‘yan sanda, da kamfanin NOAC.

Ana cin kudin fansho a Najeriya

A makon nan shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa kudin fanshon da aka sace a Najeriya a 'yan shekarun nan ya haura Naira Biliyan 150.

Shugaban na EFCC yace 70% na fanshon Bayin Allah yana fada wa cikin aljihun wasu miyagun mutane. Mista Bawa ya sha alwashin kawo karshen wannan barna.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN