Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano


Shugaban kungiyar kiristocin Nigeria, CAN, Ayokunle da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar sun bukaci ‘yan sanda su kama wasu batagari musulmai bisa halaka wani Fasto da su ka yi a Kano.

Sai da suka babbaka gidan faston, cocin da yake wa’azi da makarantar da yake kula da ita.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, a wata takarda wacce sakataren kungiyar, Cornelius Omonokhua ya sa hannu, ya nuna alhininsa akan kisan faston da farmakin da aka kai gidan sa, inda ya ce babu adalci a lamarin.

Ya kara da cewa wajibi ne a yi adalci yayin da ake neman kwantar da tarzomar a yankin.

Sun halaka faston sannan su ka kona ma sa gidan sa

Bisa ruwayar SaharaReporters, takardar ta zo kamar haka:

“NIREC, bisa shugabancin Mai girma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, Shugaban kungiyar harkokin addinin musulunci (NSCIA) da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), Rev. Dr Samson Olasupo Adeniyi Ayokunle, sun samu mummunan labari daga kungiyar CAN, reshen jihar Kano, a ranar Laraba, 22 ga watan Satumban 2021 akan yadda wasu matasa su ka halaka Fasto Shu’aibu Yohanna a anguwar su da ya kai shekaru 10 yana wa’azi a matsayin fasto.

“NIREC ta yaba da shugaban CAN, reshen jihar Kano da mataimakin shugaban CAN, na karamar hukumar Sumaila bisa jajircewar su akan lamarin don gudun ci gaba da tayar da husuma.

“NIREC ta yi allawadai da halaka Faston, farmakin da aka kai cocin , makarantar, ofishin malaman makarantar da kuma lalata gidansa da batagarin su ka yi. Babu dalilin wannan zaluncin.

“Don haka NIREC ta na yi wa iyalan faston ta’aziyya kuma tana yi ma sa fatan samun rahama.

“NIREC tana rokon hukumar ‘yan sanda ta yi abinda ya dace don tabbatar da wadanda su ka yi wannan kisan zalincin."

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, wani batagarin musulmi ne ya halaka Fasto Yohanna Shuaibu a Massu, wani kauye dake karamar hukumar Sumaila a jihar Kano.

Kamar yadda gidauniyar kiristoci hausawa (HACFO) ta bayyana a wata takarda, sai da su ka babbaka gidan faston har da makarantar sa.

Bisa yadda aka samu labari, wani matashin musulmi wanda ya koma addinin kirista ne ya halaka matar yayan sa yayin wani rikici. Daga nan batagarin su ka zargi faston ya na da hannu a kisan.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN