Hotunan Amarya da Ango da suka je wurin ɗaura aurensu a cikin tukunyar girki


Bisa tilas wata amarya da da angonta suka yi amfani da tukunyar girki wajen tsallake wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye yayin zuwa wurin ɗaura aurensu a ƙasar Indiya.

Hotunan waɗannan ma'aurata ya ƙaraɗe kafafen sada zumunta domin sun yi abin mamaki kasancewar ambaliyar ruwa ta mamaye tituna a gabashin Indiya.

BBC Hausa ta rahoto cewa Amaryar da Angonta sun ɗauki wannan matakin ne saboda ambaliyar da ta shafi yankinsu

Angon mai suna Akash, da kuma amaryarsa, Ashwarya, sun sha alwashin tabbatar da an ɗaura auren su duk da wannan matsala da suke fama da ita a ƙauyensu.

Ta ya suka yi amfani da tukunya?


Hotunan sabbin ma'auratan, waɗan da ma'aikatan lafiya ne, sun nuna yadda suka zauna daram a cikin tukunya domin wuce wuraren da ruwan ya mamaye.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan sama mai ƙarfi ya haifar da ambaliya a yankin jihar Kerala, mutane sun mutu da dama.

Ma'auratan sun nemo tukunyar ne a wurin Bauta, sannan suka nemi taimakon wasu mutane da zasu rinka tura su tamkar kwale-kwale.

Ba zamu taba mantawa da wannan lokacin ba - Ashwarya

Amaryar ta bayyana cewa sam ba su yi tsammanin bikinsu zai kai haka ba, domin ya wuce duk wani tunanin su.

Amaryar tace:


"Da fari mun tsara bikin mu da mutane yan kaɗan, amma sai ga shi ya kasance bikin da ba zamu iya mancewa da shi ba."

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN