Wata kyayyawar budurwa ta harbe saurayinta har lahira saboda ya ƙi sumbatar ta


Wata budurwa a ƙasar Amurka ta ɗirkawa saurayi harbi har lahira saboda ya ƙi ya sumbace ta.

Aminiya ta rahoto cewa, kyakkyawar budurwar ta nemi saurayin ya sumbace ta amma sam ya ƙi cika mata bukatarta.

Lamarin ya faru ne yayin da muaten biyu suke tsaka da holewarsu a gidan saurayin, suna shan barasa.

Budurwan mai suna Claudia Resendiz-Florez, yar shekara 28 ta ɗauki wannan matakin ne bayan ta nemi saurayin ya sumbace ta amma sai ya juya ya sumbaci wata budurwarsa

Yadda lamarin ya faru

Budurwar ta nuna masa fushi bayan ƙin sumbatar ta a karo na farko da ta nema, sannan ta ce ya zama wajibi ya yi abinda take so a karo na biyu.

Da saurayin yaƙi yin abinda take so a karo na biyu, nan take ta fusata, ta ɗakko bindigarsa dake ajiye a gefe guda ta harbe shi a ƙirji.

Rahoto ya bayyana cewa saurayin bai jima ba ya ƙarasa mutuwa kasancewar harsashin bindigar a ƙirji ya same shi.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Jami'an yan sanda sun cafke budurwar bayan samun rahoton abinda ya faru, kuma suna cigaba da gudanar da bincike.

Ɗan sandan dake jagorantar lamarin ya tabbatar da cewa za'a cigaba da tsare budurwar har zuwa lokacin da Alƙali zai yanke mata hukunci.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN