Har yanzu daliban FGC Birnin Yauri a Kebbi basu dawo gida ba, dan jarida ya amsa tambayoyin jami'an tsaro ya koma gida


Bayan bullar Labarin cewa Yan bindiga sun sako dalibai da suka sace a makarantar FGC Birnin Yauri ranar 13 ga watan Oktoba, har yanzu daliban basu iso ba.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa jami'an tsaro sun gayyaci dan Jaridar da ya fara wallafa Labarin sako daliban, wanda hakan ya sa sauran jaridu da kafafen watsa labarai suka dauki labarin tare da dangana asalin Labarin da Jaridar.

Kazalika mun samo cewa bayan wani lokaci a ofishin jami'an tsaro da ke Gwadangaji, dan Jaridar ya dawo gida.

Sai dai har yau ba a gan daliban ba ko inda suke. Komabayan jita-jitan da ke yawatawa cewa yaran suna Asibitin garin Kalgo.

Shafin isyaku.com ya yi tattaki zuwa Kalgo, kuma ya gano cewa yaran basu Asibitin Kalgo kamar yadda ake yayatawa.

Sai dai har yanzu, mahukunta a jihar Kebbi basu fitar da wani bayani ba da ke gaskata ko musanta zancen a kafar da aka saba samun sakonninta zuwa ga jama'ar jihar Kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN