Tashin hankali: Duba abin da ya faru bayan saurayi mai shekara 25 ya kama dan shekara 50 tare da budurwarsa a cikin daki suna ...


Jami'an yan sandan jihar Ogun sun damƙe wani matashi ɗan shekara 25, Bisi Omoniyi, bisa zargin kashe abokin takararsa a ɗakin matar da suke nema.

Dailytrust ta ruwaito cewa jami'an sun samu damar kama wanda ake zargin ne bayan kiran gagawa da aka musu ta caji ofis ɗin dake Owode Egbado.

A rahoton da yan sandan suka samu, an bayyana musu cewa wani matashi ya sheƙe wani mutumi da adda a garin Ajilete dake karamar hukumar Yewa ta arewa, jihar Ogun.

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa manema labarai cewa bayan samun wannan rahoto ne, nan take DPO Owode Egbado da CSP Olabisi Elebute, suka tura jami'an sintiri yankin, suka cafke matashin.

Yace da farko an yi gaggawar kai mutumin da aka sara da adda zuwa Asibiti, amma daga baya likiti ya tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Oyeyemi ya ƙara da cewa a binciken da yan sanda suka gudanar sun gano cewa wanda aka kashe Akinyemi Wahab, ya ziyarci ɗaƙin abokiyar baɗalarsa, Kafayat Sakariyau, domin kwana a ɗakinta.

Yace wanda ake zargin, shima yana neman wannan matar, ya kawo mata ziyara kamar yadda ya saba domin rage dare amma sai aka hana shi shiga.

Yadda lamarin kisan ya faru?

Kakakin yan sandan yace:

"Ganin an hana shi shiga ya ɓata masa rai, ya ɓalle kofar da karfin tsiya ya shiga, amma yanayin da ya tsinci budurwar tasa da mutumin ba zai iya jurewa ba, kamar yadda ya faɗa."

"Daga nan sai suka fara kokawa tsakaninsu, matashin ya ɗauki adda a ɗakin ya kafta masa sara, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa."

"A halin yanzun an kai gawar ɗakin aje gawarwaki, yayin da matar da aka aikata kisan a kanta ta tsere, ba'a san inda ta yi ba."

A wani labarin kuma Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Wani magidanci a ƙasar Indiya ya nemi a raba aurensa da matarsa shekaru biyu da aure, saboda bata yin wanka kullum.

Sai dai labarin baiwa matar ɗaɗi ba, inda ta garzaya wurin wata ƙungiyar kare mata, tana neman a ceto mata aurenta.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN