Type Here to Get Search Results !

Duba hotunan wata mata da aka kama da bindiga da harsashi da ɗimbin muggan ƙwayoyi a Najeriya


Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai sun kama wata Blessing Oghule da bindiga, sauran miyagun makamai da kuma miyagun kwayoyi. Bisa ruwayar LIB, mai magana da yawun rundunar, DSP Bright Edafe ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba. 

A cewar kakakin: “A ranar 21 ga watan Oktoban 2021 da misalin karfe 2:15, bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, CP Ari Muhammad, rundunar ta kai samame wuraren Abraka a Asaba.” Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa, a wurin an kama mutane 5 da ake zargin barayin waya ne, wata jaka da wani abu da ake zargin hodar ibilis ce da kuma wiwi duk a hannun Oghule. 

Yayin samamen, an kama mutane 4, ciki akwai Blessing Oghule, Nweke Abudi, Ebuka Paul da Sunday Inuse. A hannun su an samu bindiga karama, miyagun makamai 5, wayoyi 5 da ake zargin na sata ne, wata jaka mai dauke da wani abu mai kama da wiwi. Har ila yau a cikin jakar akwai wata leda wacce ake zargin hodar ibilis ce a ciki duk daga hannun Blessing Oghule. Legit Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies