Type Here to Get Search Results !

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a Neja


Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja, inda suka kashe wasu masallata 18.

An tattaro cewa, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne da yawan gaske inda suka far wa mutanen kauyen da ke gudanar da sallar asuba.

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Taswirar jihar Neja | Hoto: channelstv.com Source: UGC

Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim-Matane ya tabbatar wa jaridar The Nation harin.

Ya ce an kashe mutane 16 a masallacin yayin da wasu ‘yan bindiga suka kashe daya a kauyen Kaboji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Matane ya ce gwamnatin jihar ta tura tawagar jami’an soji zuwa dajin domin kamo ‘yan bindigar da ke boye a can.

Shugaban karamar hukumar Mashegu, Alhassan Isa Maza-Kuka shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya yi matukar tayar da hankali ga jama’a.

Ya ce harin ya yi muni ganin yadda jama’a ke cikin masallacin domin yin sallah.

Mista Alhassan ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda suka jikkata yana cikin mawuyacin hali kuma an garzaya da shi babban asibitin Minna domin kula da lafiyarsa.

Karin bayani na nan tafe...

Source: Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies