Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun shiga ganawar sirri a wurin babban taron jam'iyyar da ke gudana yanzu haka a Abuja.
Taron na kwana biyu, ana gudanar da shi ne a dandalin Eagle Square kuma ba za a tashi ba har sai an zaɓi shugabannin jam'iyyar a muƙamai daban-daban a mataki na ƙasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na cikin gwamnonin da ke yin ganawar. Kazalika tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Kwankwaso na cikin ganawar.
Rubuta ra ayin ka