Yanzu yanzu kai tsaye: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP


Bayan yunkurin hana taron gangamin da tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus, yayi a kotu, akalla wakilai 3600 sun taru a farfajiyar Eagle Square. Hakan ya biyo bayan watsi da karar Uche Secondus ranar Juma'a a kotun daukaka kara.

Wannan taro zai gudana tsakanin ranar Asabar, 30 ga Oktoba da Lahadi, 31. A wannan taro, za'a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar da zasu ja ragamar lamura a nan gaba. Kimanin kujeru 21 za'a dabe kuma an tantance mutane 27 da zasuyi takaran wadannan kujeru, kamar yadda Legit ta tattaro muku. 

Shugaban wannan taron gangami wanda shine gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa kujeru uku kadai ya rage ba'ayi ittifaki kuma aka yarje wadannan zasu haye ba. Kujerun sune na mataimakin jam'iyyar (na Kudu), shugaban matasa da Odito Janar. 

Zamu kawo muku rahotanni kai tsaye idan aka fara taron.
 
Legit
Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN