Da duminsa: An yi yunkurin juyin mulki a kasar Sudan, duba abin da ke faruwa


Wasu rahotanni da ke fitowa daga Sudan na cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar.

Rahotanni sun ce wasu sojoji da ba a tantance ko su waye ba sun yi wa gidan firaminista Abdallah Mandok kawanya.

Rahotanni na cewa dakarun kasar sun cafke 'yan majalisar ministocin gwamnatin hudu, da kuma farar hula daya mamba a cikin gwamnatin hadaka.

Har wa yau, an bada rahoton cafke mai bai wa mista Hamdok shawara kan harkokin yada labarai.

Kungiyar kwararru a Sudan sun yi kira ga jama'a da su fito kan tituna domin nuna bijirewa juyin mulki.

A ranar Alhamis, dubban 'yan kasar suka cika titunan birnin Khartoum domin nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya.

Dakarun Sudan da kuma shugabannin fararen hula a kasar ba sa ga maciji da juna.

Dukkan bangaroirin biyu na cikin gwamnatin hadaka tun shekarar 2019, abin da ke nuna cewa suna share fagen gudanar da zabuka a kasar.

A ranar Alhamis, dubban mutane sun yi zanga zanga a sassan kasar domin nuna goyon baya ga mulkin dimokradiyya.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN