Rahotanni sun bayyana cewa miyagun yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 6, sun yi awon gaba da wasu a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina.
Jaridar Premium Times tace maharan sun kai harin ne ƙauyen Unguwar Samanja dake ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina. Jihar Katsina dai, itace jihar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito kuma tana fama da hare-haren yan bindiga.
Yadda lamarin ya faru
Mazauna Daudawa dake makwaftaka da ƙauyen, sun shaidawa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 5:49 na yamma, lokacin da mutane ke shirin sallan Magrib.
Ƙaramar hukumar Faskari, na ɗaya daga cikin yankunan dake fama da yawaitar hare-haren yan bindiga a jihar Katsina.
Kuma Faskari tana ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 13 da gwamnati ta ɗauki matakin datse hanyoyin sadarwa domin magance matsalar.
Wata ƙungiyar al'umma dake garin Daudawa, ta koka cewa duk da matakan da gwamnatin jiha ta ɗauka, har yanzun yan bindiga na cigaba da ta'addanci a Faskari.
Harin ya yi muni sosai
Wani mazaunin Daudawa, Nasir Hassan, yace maharan sun shiga ƙauyen ne akan mashina mintuna kaɗan kafin Magrib, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Yace:
"Daga labarin da na samu, mutum 5 sun mutu, kuma an gudanar da jana'izarsu ranar Litinin da safe."
"Sun kuma ƙone gidaje da shagunan mutane kafin su fita kauyen, an faɗa mun ba su saci komai ba, sun dai ƙona shaguna."
Hassan wanda É—alibin makarantar gaba da sakandire ne a Zamfara, yace maharan sun yi awon gaba da mutane amma bai san adadin su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da masu bauta mutum uku kuma sun nemi miliyoyin kuÉ—in fansa.
Rundunar yan sandan jihar tace jami'anta sun bazama neman maharan tare da ceto mutanen da aka sace.
Kaduna - Daily Trust ta ruwaito cewa, Mai martaba Sarkin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Alhaji Zubairu Jibril MaiGwari, ya ce rufe hanyoyin sadarwa ya raunana tare da rage karfin ‘yan bindigar da ke addabar jama’a a jihar.
Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ma’aikatar tsaron da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna ta shirya.
Ya ce matakan da gwamnati ta dauka na dakile ayyukan ‘yan bindiga na samar da sakamako mai kyau a sassan karamar hukumar Birnin Gwari.
A cewarsa, hare-haren da sojoji ke ci gaba da yi a Zamfara sun fatattaki wasu ‘yan bindigar zuwa sassan Birnin Gwari saboda yunwa.
A kalamantsa:
“Mafi yawansu (’yan bindigan) da aka fatattake su daga Jihar Zamfara sun dawo Birnin Gwari sun hana mutane noma. Yanzu idan suka sace wani, sai su ce masa ya zo ya kawo musu abinci."
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an dauki matakan dakile barnar ne domin kare lafiyar jama’a don taimakawa jami’an tsaro a yakin da suke yi da ‘yan bindiga.
A baya, gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarar katse hanyoyin sadarwa a wasu sassan jihar saboda yawaitar hare-hare na 'yan bindiga, ciki har da Birnin Gwari.
Channels Tv ta ruwaito cewa, gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin durkusar da karfin 'yan bindiga a wasu sassan Kaduna.
Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro
A wnai labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce abubuwa daban-daban ne suka jawo matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
Ya yi wannan jawabi ne a wani takaitaccen biki da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, inda Jakadun Japan, Tarayyar Turai, Burundi, Denmark, Finland, Ireland, Cape Verde, Faransa, Qatar; da manyan kwamishinonin kasar Saliyo da Ghana suka karbi wasikun amincewa.
Ya ce ana bukatar karin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Source: Legit