Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa a Najeriya


Hukumar Kula Da Yadda A Ke Kashe Kudin Kasa wato (Fiscal Responsibility Commission) ta karrama Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a mastayin jajirtaccen shugaba a fannin gudanar da gwamnati a bayyane kuma bisa amana da kuma yadda yake alkinta kudaden Jiha wajen gudanar da ayyukan cigaban al'umma.

Hukumar ta ce ya zama dole a yabawa Gwamnan bisa rawar gani wajen gudanar da mulki wanda yake a bude da kuma amfani da kudin gwamnati wajen samar da ababan more rayuwa ga ‘yan jihar.

Shugaban hukumar, Barrister Victor Muruako ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jiga-jigan Hukumar su ka kai wa Gwamnan ziyara a ofishinsa da ke fadar gwamnati a yau Litinin.

Gwamna Ganduje ya yi maraba da jami'an hukumar sannan ya yaba musu bisa shirya taron wayar da kai akan tsantseni da rikon amana wajen sarrafa kudaden gwamnati sanar ya bayyana aniyar sa ta yin aiki da su.

A lokacin ziyarar Gwamnan yana tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Hon. Ali Haruna Makoda da kwamishinoni da shugaban riko na Hukumar Karbar Korafe Korafe, Barr. Balarabe Mahmud da sauran jami'an gwamnati.

Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa a Najeriya

Gwamnan jihar Kano ya samu lambar yabon zakaran yaki da rashawa a Najeriya Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Source: Facebook


Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN