Yan Bindiga Sun Kai Hari Gonar Obasanjo


Yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu ma’aikata a gonar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a garin Kobape da ke jihar Ogun. Rahotanni sun ce maharan sun faki mutanen ne, tare da budewa motarsu wuta, kana daga baya suka yi awon gaba da su. Jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.

Ba a bayyana sunayen mutanen da aka sace ba, amma manyan jami’an katafariyar gonar tsohon shugaban kasar ne. Zuwa yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro kan faruwar lamarin.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari