Yan Afghanistan na ci gaba da yi wa Taliban wani abin ban haushi


Ana ci gaba da zanga-zanga a Afganistan, a wani mataki na bijirewa dokar hana zanga-zanga da gwamnatin Taliban ta sanya.

Ministan harkokin cikin gida na Taliban ya ce an dauki matakin ne saboda wasu mutane na amfani da zanga zangar don janyo matsalar tsaro da kuma haifar da hargitsi.

A cikin kwarin Panjshir,rahotanni sun ce mayakan Taliban din sun wulakanta kabarin shahararren jagoran masu adawa da Taliban Ahmed Shah Massoud a bikin cika shekara 20 da kasheshi.

Jami’an Amurika sun ce kimanin yan Amurika 200 da yan kasashen waje na shirin barin Kabul a cikin jirage masu saukar ungulu da yammacin yau, bayan Taliban ta amince da kwashe su.

Rahotun BBC

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN