Akan kalli fina-finai domin nishadi da debe kewa, hakazalika da ma bata lokacin zama ba aikin komai, amma kun taba tunanin akwai fim din da zaku kalla kuma a biya ku ku kudade?
Wani kamfanin hada-hadar kudi zai ba da $1,300 (N534,950.00) ga duk wanda ke son zama ya kalli wasu manyan fina-finai masu ban tsoro da aka taba yi a duniya.
Manufar yin haka
A cewar CNN, kamfanin mai suna FinanceBuzz yana bincike ne don sanin ko girman kasafin kudin fina-finan yana tasiri da yadda tasirinsa yake ga masu kallo.
Kamfanin zai yi hayar wani don ya zama mai yin duba da lura kan bugun zuciya, kuma yayin da mutum ke kallon fina-finan, za a kula da bugun zuciyarsa ta amfani da na'urar Fitbit don gano wasu abubuwa.
Jerin sunayen fina-finan
Wasu daga cikin sunayen fina-finan na sanya mutum mai saurin tsorata shiga wani yanayi na tsoro.
Ga fina-finan kamar haka:
Get Out
Halloween(2018)
Saw
A Quiet Place
Insidious
Amityville Horror
A Quiet Place Part 2
The Purge
Candyman
The Blair Witch Project
Annabelle
Sinister
Paranormal Activity
Yadda za a shiga tsarin
Za a bubaci duk wanda aka zaba ya kalli fina-finan 13 tsakanin 9 ga Oktoba zuwa 18 ga Oktoba.
Kamfanin zai bai wa manazarcin da zai kula da shirin na'urar Fitbit, kudaden lada da kuma wasu karin $50 (N20,575).