Duba manyan sarakunan da 'yan bindiga suka sace a arewacin Najeriya


Kai wa sarakuna tare da sace su a wasu lokutan na zama ruwan dare a Najeriya musamman arewacin kasar, tun bayan da hare-haren 'yan bindiga da masu satar mutane don kudin fansa suka yi kamari.

Na baya-bayan nan shi ne sace Sarekin Bungudu na jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar da aka yi a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Ga dai jerin wasu sarakuna na yankin arewacin kasar da 'yan bidnga suka sace, duk da cewa duk an sako su in ban da na Bungudun.

Sarkin Bungudu

A ranar Talata da yamma ne wasu ƴan bindiga suka sace Sarkin Bungudu da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

Ƴan bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda BBC ta ji daga ɗaya daga cikin ƴaƴansa da kuma basarake a masarautar Zannan Bungudu Abdulmalik Zubairu.

Bayanai sun ce an kashe ɗaya daga cikin jami'in ƴan sandan da ke tare da shi a musayar wuta da ƴan bindigar a hanyar Abuja daga Kaduna.

Mai martaba Alhaji Hassan Attahiru yana cikin sarakunan Zamfara masu daraja ta ɗaya, kuma kawo yanzu ba a ji duriyar sarkin ba.

Sace sarkin wani babban ƙalubale ne musamman a daidai lokacin da aka ɗauki matakin toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwannin mako a wasu jihohin arewwaci don maganin hare-hare- da satar mutane.

Sarkin Kajuru

A ranar 11 ga watan Yuli ma yan bindiga sun sace sarkin Kajuru a jihar Kaduna Alhaji Alhassan Adamu.

An sace sarkin da wasu iyalansa su 13 a wani harin da 'yan bindigar suka kai a masarautarsa.

Bayanan da suka fito a lokacin sun nuna cewa sarkin ya gudanar da taro kwana daya kafin nan, kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.

Yan kwanaki bayan haka kuma aka sako sarkin mai shekaru 85.

Sarkin Jaba

Makonni biyu bayan sace Sarkin Kajuru ne shi ma Sarkin Jaba Jonathan Danlin Gyet Maude ya fada hannun yan bindiga.

Sai dai shi Sarki Jonathan Maude an sace shi ne yayin da ya kai ziyara wata gonarsa a yankin Panda na Jihar Nasarawa.

Masu garkuwar sun bukaci naira miliyan dari biyu a matsayin kudin fansa a lokacin.

An kuma sako shi bayan kwana guda yayin da yan binidgar suka ci gaba da tsare wasu mutum 13 da suka sace tare da shi.

Sarkin Rubochi

A watan Nuwamban 2019 'yan bindiga sun yi awon gaba da sarkin garin Rubochi da ke karkashin karamar hukumar Kuje ta Abuja.

An sace Etsu Mohammed Ibrahim Pada ne da misalin karfe biyu na daren Talata 27 ga watan Nuamban 2019 bayan da suka kutsa kai cikin gidansa.

Babu bayanai da su ka nuna cewa an biya kudin fansa ne kafin a sako shi.

Sarkin Wammako

A jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriyar an taba sace sarkin Wamakko Alhaji Salihu Baraden Wamakko a ranar 9 ga watan Maris din 2015.

Kamar Sarkin Kajuru, shi ma maharan sun dauke shi ne takanas-ta-kano a masarautarsa.

Basaraken yaya ne ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Kuma shi ma an sako shi bayan wani lokaci.

Sarkin Bukkuyum

Har wayau a ranar 21 ga watan Maris din 2015 mahara sun sace Sarkin Bukkuyum mai Martaba Alhaji MUhammadu Usman a jihar Zamfara.

'Yan bindigar sun sace sarkin a masallacin kofar gidansa bayan Sallar Magriba ranar wata Juma'a.

Kafin nan sai da suka yi harbe-harbe na tsorata jama'a kafin su yi awon gaba da sarkin mai daraja ta daya.

Sai dai kasa da mako guda da garkuwa da sarkin ne yan bindigar suka sako shi.

Yunkurin sata ba nasara

To amma yayin da mahara suka yi nasarar garkuwa da wasu sarakunan, an samu wadanda suka sha da kyar yayin kai musu harin.

Sarkin Potiskum

A watan Janairun 2020 wasu mahara sun kai wa Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, hari inda suka kashe mutum shida, kamar yadda rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana.

Kakakin Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna DSP Yakubu Abubakar Sabo ya ce abin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, a kusa da garin Marabar Jos da misalin karfe 11:00 na daren ranar Talata.

Ya ce wasu mahara ne suka bude wa ayarin motocin sarkin wuta wanda hakan ya yi ajalin mutum shida - biyu fasinjoji da ke tafiya a hanyar, hudu kuma daga cikin jama'ar sarkin.

Sarkin Potiskum babban sarki ne a masarautarsa da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Sarki Kaura-Namoda

A ranar 12 ga watan Disamban bara ne 'yan bindiga su ka kai wa tawagar motocin Sarkin Kaura-Namoda Alhaji Sunusi Muhammad da ke jihar Zamfara farmaki kan hanyarsa ta dawowa Gusau daga Zaria.

Maharan sun yi wa jerin motocin kwanton bauna inda suka hallaka akalla mutane takwas tare da jikkata wasu mukarrabansa.

Daga cikin wadanda suka kashe akwai direba guda da kuma 'yan sanda uku. Sai dai Sarkin na Kaura Namoda ya tsira ba tare da samun rauni ba.

Sarkin Birnin-Gwari

A watan Maris din wannan shekarar ma mahara sun buda wa tawagar sakin Birnin-Gwari ba II Alhaji Zubairu Jibrin wuta.

Harin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sai dai sarkin baya cikin motar tasa a lokacin harin na 17 ga watan Maris, wanda ya sa ya shaida wa BBC cewa an turo a kashe shi ne ba a san cewa baya cikin motar ba.

Kuma a cewarsa yaana zargin akwai hadin baki da wasu daga masauratar tasa.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE