Rahotu kan yadda jama'a ke karanta labaran gidan gwamnatin jihar Kebbi


Rashin fassara Labaran ababen da ke faruwa a fadar Gwamnatin jihar Kebbi (Press Release) zuwa harshen Hausa a ko da yaushe yana kawo gibi na sanin ainihin abin da ke faruwa a cikin jiha ga mafi yawan talakawa a jihar Kebbi.

Wani bincike da shafin labarai na isyaku.com ya gudanar ya nuna cewa kaso 20% na jama'ar jihar Kebbi ke karanta Labaran ababen da ke faruwa a gwamnatance wanda mai taimaka wa Gwamna kan harkar labarai Yahaya Sarki da Sakataren watsa labarai na gidan Gwamnati Abubakar Muazu Dakin gari ke rubutawa da harshen Turanci.

Rahotun ya ce ko a cikin kaso 20% na wadanda ke karantawa,  kaso 10%  yan Boko ne mazauna garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi, yayin da sauran kaso 10% ke karantawa a sauran sassan jihar Kebbi.

Kazalika binciken ya nuna cewa kaso 70% ne suka karanta labarin gidan Gwamnatin jihar Kebbi da shafin isyaku.com ya fassara kuma ya wallafa da harshen Hausa. Tsari da aka yi amfani da kimiyyar tantancewa da nazari na kamfanin Google Analytics.

Tuni dai shafin isyaku.com mai asali da jihar Kebbi ya labarta wa mai taimaka wa Gwamnan jihar Kebbi kan harkar labarai Yahaya Sarki kan muhimmancin fassara labarai da yake wallafawa ta hanyar amfani da yan Jarida na ma'aikatar watsa labarai na jihar Kebbi da ke gidan Gwamnatin jihar Kebbi.

Yan watanni baya dai, Mawallafin shafin isyaku.com ya shawarci mahukunta a jihar Kebbi kan sakamakon rahotun bincike kan lamarin. Da kuma yadda za a isar da sakon Gwamnati ga talakawan jihar Kebbi da harshen gado domin wadatar da Talakawan jihar da ingantattun labarai kan lamurran da ke faruwa a jihar a hukumance.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN