An sace saurayi da budurwa ana gab da shagalin bikin aurensu


Rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti ta damke wasu mutum uku da zargin hannu a sace wani mutumi da matar da zai aura suna cikin shirye-shiryen biki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa an sace masu shirin zama ma'auratan ne a kan hanyar Ilasa- Ayebode dake ƙaramar hukumar Ekiti ta gabas, ranar Lahadi.

Lamarin ya faru da masoyan biyu ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Ado Ekiti, babban birnin jihar, inda suka je siyayyar bikin aurensu.

Mutanen sun nemi a biya kuɗin fansa

Maharan da suka yi garkuwa da saurayin da budurwarsa sun tuntuɓi iyalansu, inda suka nemi a tattara musu naira miliyam N5m a matsayin kuɗin fansa.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da kame mutum uku da ake zargi da hannu dumu-dumu a lamarin.

"Waɗanda aka sace ɗin suna tsaka da shirye-shiryen aurensu. Sun je Ado Ekiti domin yin siyayyar wasu abubuwa, kuma a kan hanyarsu ta komawa gida ne wasu yan bindiga suka yi awon gaba da su."

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari