Mahaifi ya kaura wa diyarshi mai shekara 17 cikin shege, duba dalili


An ceto wata yarinya Yar shekara 17 bayan mahaifinta ya yi mata cikin gaba da fatiha kuma ya kore ta daga gida a garin Eket a jihar Akwa Ibom. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Wani ganau mai suna Oga Yenne, ya ce an gan yarinyar ne a Unguwar Plaza a birnin Uyo tana neman wanda ke bukatar Jariri da ke cikinta ranar Talata 21 ga watan Satumba.

Yarinyar ta yi zargin cewa mahaifinta ne yake kwanciya da ita har ta dau ciki. Ta ce mahaifinta ya fara kwanciya da ita ne tun lokacin da mahaifiyarta ta mutu.

Previous Post Next Post