Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya yi imanin cewa hanya guda da zai bi wajen kawo canjin da ake so a Najeriya shi ne shiga siyasa da kuma yiwuwar shiga takarar shugaban kasa a 2023.
Ana kyautata zaton Jega zai tsaya takara a jam'iyyar Rescue Nigeria Project (RNP) tare da wasu manyan masu sharhi kan al'amuran yau da kullum kamar Pat Utomi da Donald Duke, tsohon gwamnan Kuros Riba.
Jega na da ra'ayin cewa rushe tsarin jahohi 36, da sake daidaita jihohin zuwa yankunan siyasa na kafin shekarar 1966, ko ma zuwa jihohi 12 na zamanin 1976/77 yana daya daga cikin mafi dacewa a hanyoyin fitar da ci gaba cikin sauri a fadin kasar nan.
A yayin taron farko na kungiyar RNP a Abuja a ranar Litinin, 20 ga Satumba, Jega ya lura cewa maganganun da ake a yanzu na kirkirar wasu jihohi wani yanki ne na nuna wariya a wasu yankuna.
A cikin shawararsa, Jega ya ba da shawarar cewa soke wasu jihohi, akalla 24 daga cikin su, za su kasance abu mai yiwuwa da fa'ida.
Daily Trust ta ruwaito shi inda yake kushe yunkurin da wasu ke yi na taso da maganar kara jihohi a Najeriya su kai 42.
Jerin jihohin da za a soke su a Najeriya
Idan RNP ta ci nasarar karbe ragamar Najeriya, a kasa ga jerin jihohin da za a soke su daga 2023.
1. Abia
2. Adamawa
3. Akwa Ibom
4. Anambra
5. Bayelsa
6. Borno
7. Delta
8. Ebonyi
9. Edo
10. Ekiti
11. Enugu
12. Gombe
13. Jigawa
14. Katsina
15. Kebbi
16. Nasarawa
17. Ogun
18. Ondo
19. Osun
20. Oyo
21. Sokoto
22. Taraba
23. Yobe
24. Zamfara
Legit Nigerian
Rubuta ra ayin ka