Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC


Akwai kwararan dalilan da suke ta dakatar da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan daga komawa jam’iyyar APC mai mulki a kasa.

Sahara Reporters ta ruwaito yadda manyan ‘yan jam’iyyar APC masu juya mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari suke son janyo Jonathan zuwa jam’iyyar APC don kada burin jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu na zama shugaban kasa a shekarar 2023 ya tabbata.

Ana tsaka da yada rahotanni akan burinsa na komawa APC daga jam’iyyar PDP, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dan dakata ne sakamakon wasu sharuddan da yake jira APC ta cika.

SaharaReporters ta bayyana yadda baya ga wannan dalilin, masu juya mulkin Muhammadu Buhari suke fargabar son kawo Jonathan don su lalata shirin jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu na zama shugaban kasan Najeriya a 2023.

Wata majiya mai karfi ta sanar da SaharaReporters cewa Buhari ya yita neman Jonathan ya koma APC tun 2020 don ya maye gurbin sa idan ya sauka.

Majiyar ta ce, ‘yan fadar shugaban kasa suna so Jonathan ya dare mulki bayan Buhari ya sauka don sun san ba zai tsananta binciken lamurran da suka auku ba a lokacin mulkin Buhari.

Kowa ya san yadda Jonathan ya dade yana so ya koma kujerar don kammala karon sa na 2, damar da APC ta hana shi sakamakon mummunan kayen da ta yi masa a zaben 2015.

Sai dai ya hakura ya mika wuya musamman ganin cewa baya da tabbacin tsayawa takara a PDP musamman ganin yadda tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya fi shi kudi da sanin jama’a yake da burin tsayawa takara.

Duk da Atiku bai bayyana ra’ayin sa na tsayawa takara ba, Jonathan ya na zullumi

A zaben 2019, dama Atiku ne ya tsaya takarar shugabancin kasa a lokacin. Duk da dai har yanzu Atiku bai tsaya ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takara a 2023 ba amma akwai alamun hakan.

Sannan Jonathan yana fargaban yadda gwamna Tambuwal na jihar Sokoto da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers suke kokarin tsayawa takara a jam’iyya PDP, ko wannan ma kalubale ne a gare shi.

Don haka ne har yanzu Jonathan ya bai wa masu juya gwamnatin Buhari wasu sharruda da har yanzu basu riga sun cika ba shiyasa har yanzu bai koma jam’iyyar APC ba.

Jonathan ya san da kyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023

Kamar yadda majiyar ta ce:

“Kusan shekara daya kenan da Jonathan ya fara tuntuba yana neman yadda ze yi ya koma APC. Jonathan ya san cewa da kyar ya samu damar tsayawa takara a PDP sakamakon yadda Atiku, wanda ya fi shi mutane da dukiya yake neman kujerar sannan Tambuwal da Wike ma su nuna ra’ayin su akan tsayawa takarar."

Ganin yadda masu juya mulkin Buhari suke so su jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato su tunkudar da burin Tinubu na maye gurbin Buhari a 2023 sannan su maye shi da Jonathan wanda za su ci karen su babu babbaka yasa ya dakata har zuwa wani lokaci.

Majiyar ta kara da cewa:

Buhari da masu jiya mulkin sa suna so su dakatar da takarar Tinubu su dauki Jonathan.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN