Ku kashe yan bindiga ko da sun shiga cikin jama'a - Gwamna ya gaya wa soji


Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya roki sojoji kada su tausaya wa yan bindiga ko ina suka gansu, su buÉ—e musu wuta, kamar yadda Amniya Hausa ta ruwaito.

Gwamnan yace matakan da aka ɗauka sun jefa rayuwar yan bindigan cikin mawuyacin hali, inda a yanzun suke ƙoƙarin shigowa cikin mutane

Amma Masari ya bukaci dakarun sojojin kada su tausaya musu koda sun shiga cikin mutane a bude musu wuta, ko da hakan zai ritsa da mutanen da ba ruwansu.

Sai dai Masari ya roki jami'an sojin su É—auki wasu matakan kariya ga mutanen idan irin haka ta faru, gudun kashe waÉ—anda ba ruwansu da yawa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Masari ya yi wannan furucin ne yayin da ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ziyarce shi, domin samun bayanai kan irin nasarorin da ake samu a yaƙi da yan bindiga.

Ba maganar sulhu da yan ta'adda

A nasa É“angaren, Ministan yace:

"Daga yanzun gwamnatin tarayya ba zata amince da yin sulhu da yan bindiga da yan ta'adda ba."

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, yace ba dai-dai bane tattaunawar sulhu da irin waÉ—annan mutanen.

WaÉ—annan mutanen ba su da addini, ya kamata a haÉ—a karfi da karfe kuma a É—auki duk matakan da ya dace domin kawar da su baki É—aya."

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN