Da duminsa: Makwabci ya kama dan acaba mai kai yaran makwabcinsa makaranta yana lalata da mahaifiyarsu, duba yadda lamarin ya faru


Makwabcin wani ma'aikacin banki a birnin Enugu ya kama wani dan acaba yana lalata da matar makwabcinsa da rana tsaka ranar Laraba 15 ga watan Satumba.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa rahotanni sun ce dan acaba da aka kama da matar ma'aikacin bankin shi ne yake kai yaran gidan makaranta kuma ya dauko su idan sun tashi daga makarantar.

Sai dai rana ta bace wa dan acaba ne lokacin da makwabci ya bi wani maciji da ya bi ta bangon da ke tsakanin gidansu da na ma'aikacin bankin domin ya kashe shi, sakamakon haka ya haura katangan.

Yin haka ke da wuya sai ya gan dan acaban turmi tabarya kan matar makwabcinsa yana lalata da ita bayan sun shimfida wani karamin katifa a dan filin da ke tsakanin ginin katangar da ginin gidan makwabcinsu.

Cikin rudani dan acaba ya bude kofar shingen gidan ya fita waje da gudu, ya mance bai sa wando ba. Ganin fitowarsa ba wando ya sa jama'a suka tuhume shi, sai dai ya gaya masu gaskiya abin da ke faruwa tsakaninsa da matar maigidansa bayan sun yi masa dukan fitar hankali.

Kawo yanzu dai babu karin bayani kan halin da dan acaba yake ciki balle makomar matar da mijinta sakamakon wannan lamari. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN