Da duminsa: Direba ya banke dan KAROTA, ya kara wa wandonsa iska


Wani direba da ba a san ko waye ba a jihar Kano ya banke tare da kashe jami'in hukumar kula da lamurran tituna, KAROTA da ke titin BUK a tsakiyar birnin Kano.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, direban ya tsere bayan ya banke jami'in KAROTA kuma abokan aikinsa sun yi kokarin cafkarsa amma abun ya gagara.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun KAROTA, Nabilusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an mika gawar jami'in asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Abubakar ya ce ba zai iya kara cewa komai ba game da lamarin saboda hukumar na jiran rahoton aukuwar lamarin ne daga asibitin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kara da daukan alkawarin samar da karin bayani bayan an kammala bincike

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari