Babu ruwan Gwamnatin jihar Kebbi da karin farashin shaguna daga N60, 000 zuwa N300,000 a Olumbo plaza Birnin kebbi


Bayan dan kasuwan nan Sanusi Na'Allah Jega ya kara kudin hayan shagunan kasuwarsa ta "Olumbo Plaza" daga N60, 000 zuwa N300,000 a mako da ya gabata. Lamarin ya tayar da kura tare da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin jama'a musamman ga yan kasuwar wayar salula a garin Birnin kebbi.

Idan baku manta ba, shafin labarai na isyaku.com ya labarta maku zancen rade-radin karin farashin shagunan a mako da ya gabata. 

Sai dai sakamakon bincike da shafin isyaku.com ya gudanar, ya nuna cewa wasu daga cikin wadanda suke kiran kansu shugabanni a wannan kasuwar, sun bukaci sauran masu shaguna a kasuwar su tashi lokaci daya su koma wata kasuwar a garin Birnin kebbi, inda suke zaton samun saukin kudin haya.

Sai dai wasu daga cikin masu haya a kasuwar, suna kallom cewa Sanusi Na'Allah Jega bai yi masu adalci ba cewa ya kara kudin shagunansa daga N60,000 zuwa N300,000 a lokaci daya babu sanarwar cewa zai yi haka domin bayar da dama ga yan kasuwa masu haya a shagunansa su shirya wa sabon farashin.

Gwamnatin jihar Kebbi bata da alaka da wannan lamari

Sakamakon wani bincike da shafin isyaku.com ya gudanar a garin Birnin kebbi kan lamarin, karin kudin haya a Olumbo Plaza, ya nuna cewa wasu masu shaguna a wannan Plaza tare da yan uwa da abokanansu, suna zargin kamar Sanusi Na'Allah ya dauki wannan matakin ne bisa tunanin kusantarsa da Gwamnati. 

Suna masu nuni da wani katafaren allon "fatan alkhairii"  da aka sa a kusa da gidan gyara hali mai matsakaicin tsaro na tarayya da ke kan hanyar Jega a garin Birnin kebbi, wanda ya nuna hoton Gwamna Abubakar Atiku Bagudu yana murmushi a gefe daya kuma aka gan hoton Sanusi Na'Allah. Wannan hoto ya haddasa shakka a zukatan wasu da suka mallaki shaguna a kasuwar tare da iyalansu.

Sai dai sakamakon bincike da shafin isyaku.com ya yi kan lamarin, ya tabbatar cewa wannan katafaren hoto banga ne kawai na fatan alkhairii ga Gwamna Bagudu kamar yadda kowane masoyinsa zai iya yi, amma baya da alaka da lamarin rikicin haya a Olumbo Plaza.

Kazalika, mun samo cewa babu wani jami'in Gwamnatin jihar Kebbi da ya goyi baya, ko ya daure wa abin da ke faruwa a Olumbo plaza gindi ko akasin haka.

Ko dokar haya a jihar Kebbi ta bayar da daman kara kudin haya daga N60,000 zuwa N300,000 ?

Sakamakon bahasi da bayani da muka tattaro daga majiya mai tushe dangane da haya, tsakanin mai gidan haya da mai haya a jihar Kebbi, ya nuna cewa mai bayar da haya yana da hurumin kara N50,000 ne kacal. 

Wanda ke nuna cewa kara kudin haya daga N60,000 zuwa N300,000 zai iya haifar da jayayya a gaban Kotun lamurran haya.

Me Karin kudin haya a Olumbo Plaza ke nufi?

Karin kudin haya daga N60,000 zuwa N300,000 a lokaci daya a dai-dai wannan lokaci, ya saba wa hankali, al'ada da akidar zamantakewar kasuwanci a garin Birnin kebbi bisa munufa da ma'aunin lissafin wadataccen mutunci, da'a ga rayuwa, da tarbiyyar ziciya da nazarin daidaiton zamantakewan al'ummar garin Birnin kebbi da jihar Kebbi a cewar masana.

Me dagewa da karin kudin haya a Olumbo Plaza ke nufi?

Masana na hasashen cewa wannan mataki zai iya zama wani mataki na takura wa ga yan kasuwa masu haya idan har wannan mataki ya yi nassara. 

Kazalika, masana sun yi hasashen cewa wasu yan kasuwa masu Plaza a garin Birnin kebbi, za su iya kara wa masu haya kudi haka kawai domin wani ra'ayi. Lamari da zai shafi tattalin arzikin kasuwanci a garin Birnin kebbi.

Kazalika, masana sun yi hasashen cewa kyale wannan lamari haka kawai, zai iya ja wa Gwamnati bakin jini a idanun jama'a idan har wasu masu shaguna suka bi sahun karin kudin haya da aka yi har kaso 450%.

Miye shawara ko mafita ?

Kwararrun masana kan irin wannan lamari, sun bayar da shawarar cewa Sanusi Na'Allah ya sami shawarar Kotun haya a garin Birnin kebbi, kuma ya yi aiki da shawararta. 

Idan yana da korafi kan masu haya a kasuwarsa, sai ya gabatar a gaban Kotun haya domin neman bahasi. 

Kazalika ta wannan Kotun haya ne zata iya kwato masa hakkinsa kan kowane dan haya da ya saba ka' idar haya. Ko idan yan haya ne ke zargin cewa mai Olumbo plaza ne bai yi masu dai-dai ba.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE