Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi


Akalla fursunoni 240 ne suka tsere daga Cibiyar Tsaro ta MSCC da ke Kabba, Jihar Kogi, bayan wani hari da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai, Channels TV ta ruwaito.

Mai magana da yawun ma’aikatar gidan yari (NCoS), Mista Francis Enobore ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar daren ranar Lahadi.

A cewarsa, maharan da yawansu sun isa gidan gyara halin dauke da muggan makamai kuma nan da nan suka fafata da masu gadin gidan ta hanyar musayar wuta.

Mista Enobore ya ci gaba da bayyana cewa Kwanturola -Janar, Haliru Nababa ya ba da umurnin a fara aikin kamo su nan take tare da gudanar da cikakken bincike yayin da ya jagoranci wata tawaga don tantance halin da ake ciki.

Nababa ya kuma yi kira ga jama'a da su bai wa jami'an tsaro bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen kamo wadanda suka tsere.

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa an kashe sojoji biyu da ke kan shingen bincike a gaban gidan gyara halin sannan kuma aka jikkata wani a lokacin da maharan suka kai farmaki.

Wata majiya ta tabbatar da cewa daga baya an sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsare da misalin karfe 8 na safe ranar Litinin a kusa da Otal din Kudon, Kabba, lokacin da suka yi kokarin shiga abin hawa don tserewa zuwa jihar Kwara da ke makwabbtaka.

Legit Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN