Da dumi-dumi: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro


Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da rufe makarantun sakandire na kwana 30 da ke jihar daga cikin kananan makarantu 34 saboda matsalar rashin tsaro.

Rufewar, a cewar wata sanarwa daga kwamishiniyar ilimi , Mrs. Wilbina Jackson, za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Satumba, 2021 har sai an sake samun wani ci gaba.

Sanarwar da wakilin jaridar Punch ta gani ta ce daukar wannan mataki wani yunkuri ne na tabbatar da tsaron dalibai saboda rashin tsaro da ke addabar kasar.

Da dumi-dumi: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

Matakin na gwamnatin jihar ya zo ne a yayin da ake ci gaba da samun karuwar ‘yan bindiga a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar sace daruruwan yara 'yan makaranta a jihohi da dama.

Karin bayani na nan tafe...

Source: Legit

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari