Soji sun yi juyin mulki a kasar Guinea sun kama shugaban kasa ba a san makomarsa ba


Wasu gungun sojoji a kasar Guinea sun ce sun yi juyin mulki kan shugaba Alpha Condé. BBC Hausa ta ruwaito.

Da yake jawabi a gidan talabijin na kasa, shugaban runduna ta musamman ta sojan Guinea Kanal Mamady Doumbouya, ya ce sojoji sun hamɓarar da Mr Condé, kuma sun rusa gwamnatinsa da kundin tsarin mulki.

Ya ce sun hamɓarar da gwamnatin Conde ne saboda yadda cin hanci da rashawa da talauci ya yi katutu a Guinea.

Wasu hotuna da bidiyo da aka yaɗaa kafafen sada zumunta, sun nuna wani mutum da aka kira Mr Condé ne sojoji sun zagaye shi.

Sai dai ma'aikatar tsaro a Guinea ta fitar da wata sanarwa inda ta ce jami'an tsaro sun fatattaki masu juyin mulkin.

A bara, an kashe masu zanga -zanga da dama a zanga -zangar adawa da Shugaban Guinea, Alpha Conde, bayan da ya gabatar da sauye -sauye ga kundin tsarin mulkin kasar kuma ya lashe wa'adin mulki na uku.

Babu tabbas kan makomar Alpha Condé

Ba a san makomar shugaban kasar Guinea Alpha Condé ba bayan wani faifan bidiyo da ba a tantance ba ya nuna shi a hannun sojoji, wadanda suka ce sun ƙwace mulki.

Sun fito a kafar talabijin ɗin ƙasa suna iƙirarin cewa sun rusa gwamnati.

An nuna sojoji guda tara a talabijin da ba a bayyana sunayensu waɗanda suka ce sun ƙwace mulkin.

An shafe sha'o'i ana musayar wuta a fadar shugaban ƙasa a Conakry, babban birnin ƙasar.

Wani bidiyo da BBC ba ta tantance ba, an ji sojojin na tambayar shugaba Conde ya tabbaar da cewa ba abin da ya same shi, amma kuma ya ƙi amsawa.

Bidiyon ya nuna Conde a zaune sanye da wando jeans da riga, kuma kamar babu wani alamun rauni da yake É—auke da shi.

Waɗanda suka yi juyin mulkin sun ce an rufe dukkanin kan iyakokin ƙasar.

Sai dai a cewar ma'aikatar tsaron ƙasar, dakarun da ke biyayya ga shugaba Conde sun murƙushe yunƙurin.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an kashe sojoji uku a musayar wutar da aka yi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN