Ana cikin bala'i a yankin arewa maso yammacin Najeriya — Bafarawa


A Najeriya, wani tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma ƙasaitaccen ɗan siyasa a arewa maso yammacin kasar ya koka kan yadda mutanen yankin suka noma gonakinsu amma ba za su iya zuwa su girbe amfani ba saboda barazanar tsaro.

Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce kamata ya yi gwamna Bello Matawalle, ya zagaya sassan jiharsa ta Zamfara don tantance tasirin matakan da ya ɗauka na kassara 'yan fashin daji da kuma ɓullo da matakan rage raɗaɗi ga jama'a.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci shugaba Muhammadu Buhari, da shi ma ya kai irin wannan ziyara ko ya tura wakilai don su je su tantance haƙiƙanin abin da ke faruwa yanzu a jihohin arewa maso yamma da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji.

Alhaji Bafarawa, ya ce wannan abubuwa da suke faruwa a arewacin Najeriya wani bala'i ne, saboda halin da ake ciki a jihar Sokoto da Zamfara bai misaltuwa sai dai wanda ya je ya gani.

Ya ce," Ban sani ba ko mutanen da suke fadawa shugaban kasa halin da ake ciki a wadannan jihohi a game da tsaro suna fada masa gaskiya ko akasin haka, domin idan dai har basa fada masa gaskiya to sun cucemu".

Alhaji Bafarawa, Allah ya gani suna cikin bala'i, domin shi ganau ne, saboda an yi noma a wadannan yankuna ga amfani ya yi kyau, to amma ba sa iya debowa saboda fargabar 'yan bindiga ta sa kowa ba ya iya zuwa ya debi abin da ya noma.

Tsohon gwamnan ya ce," Manoma na tsoron idan sun je dibar abin da suka noma ba lallai su dawo da ransu ba".

Ya ce ba wai maganar siyasa ya ke ba, wannan bala'i shima ta shafe shi saboda dan yankin ne, don haka a cewarsa yana da kyau shugaban kasa ya hada kwamiti ya tura su su je su ga irin abin dake faruwa a Bafarawa ma kadai ba sai sun je ko ina ba.

Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce batun cewa gwamnati ta na tallafawa da abinci, shi daibai taba gani ba, domin ko da baya zama a Bafarawa, ai yana zuwa a kai-a kai, kuma da a labari ma zai ji ko ya gani.

Ya ce," Kamata ya yi duk wani shugabaidan ya ce ya sa doka to ya rinka bibiya ya ga ko wannan doka na aiki ko bata yi, idan an ce ana bada abinci ga mutane, to a matsayinka na shugabasai ka saka kwamiti wanda zai rinkabibiya ya ga ko ana rabon wannan abinci ko akasin haka".

Tsohon gwamnan ya ce," Yakamata shugaban kasa ya sa kwamiti wanda zai je ya ga ko abin da na fada gaskiya ne ko akasin haka, sai a tantance".

Alhaji Bafarawa ya ce bayan azabar rashin abinci a yankunan da ake fama da rikicin 'yan bindiga, karatu ma ba bu, don yara basa iya zuwa makaranta saboda fargabar kada 'yan bindiga su sace su.

A donhaka ya ja hankalin gwamnatin tarayya dama na jihohin da ke fama da matsalar tsaro da su kara himma wajen inganta rayuwar al'ummarsu, domin hakki ne da ya rataya a wuyansa.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN