An yi wa yaro mai shekara 7 yankan rago a Jos ta arewa


An yi wa dan karamin yaro dan shekara 7 mai suna Abdul Ahad Nasiru yankan rago a unguwar Tudun Pera a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Plateau. 

An gano gawar yaron ne da safe a rafin Rimi da ke Angwan Rogo ranar Juma'a 24 ga watan Satumba wuyarsa a yanke. 

Mai gabatar da shiri Bello Lukman a gidan rediyon Unity Fm 93.3 a birnin Jos ya sanar da Labarin.

Ya ce an yi wa yaron ganin karshe ranar Alhamis 23 ga watan Satumba da misalin karfe 2 na rana, bayan ya dawo daga wajen wasa, sai ya sake fita, Wanda shi ne ganin karshe da aka yi masa a gida.


Previous Post Next Post