Yansandan ofishin Dention a birnin Lagos, sun kama wani mutum mai suna Oluchi Okoye aka PACA, bayan ya daure wani mutum mai suna Reuben Olozie a itace saboda ya kasa biyansa bashin kudi N4.6m da yake binshi
Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa wanda aka kama ya daure wanda yake bi bashi a gida mai lamba No. 29, Abeokuta Street, Ebute Metta, Lagos daga ranar 22 zuwa ranar 23 ga watan Satumba lokacin da yansanda suka kuɓutar da shi.
Wanda yansanda suka kama ya ce ya yi iyakar kokarin ganin wanda ya daure ya biya shi bashinsa, amma ya ki, kuma shi ya sa ya daure shi domin kudinsa ya fito.
Matar Reuben wanda ya ci bashi mai suna Angela Reuben ce ta kai kara wajen yansanda, cewa wanda ke bin mijinta bashi ya daure shi da igiya a cikin gida har tsawon kwana daya.
Kwamishinan yansandan jihar Lagos CP Hakeem Odumosu, ya bayar da umarnin cewa, a kai matsalar sashen kwararrun yansanda masu bincike na Tactical team, domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Kalli bidiyo a kasa:
Rubuta ra ayin ka