An kama wadanda suka kashe matafiya masu Zikiri a Jos, duba sunaye, da abin da zai faru


Rundunar ‘yan sanda na jihar Filato, sun gurfanar da wasu mutane 10 da ake zargin su da hannu a kashe wasu Fulani da tafiya ta bi da su ta Jos.

Jaridar Daily Trust tace an hallaka wadannan mutane ne yayin da suka bi ta titin Gada-biyu zuwa Rukuba, garin Jos, a jihar Filato a cikin tsakiyar watan Agusta.

Jami’an tsaron sun gurfanar da wadanda ake zargi da wannan laifi a babban kotun jiha da ke Filato.

Sunayen mutane 10 da aka kama

Lauyar da ta tsaya wa ‘yan sanda, Muleng Alex, tace wadannan mutane 10 sun kashe wasu matafiya da suke kan hanyarsu ta zuwa Ondo, daga garin Bauchi.

Wadanda aka gurfanar a kotu sune Mathew Daniel, Juarbe Zamani, Dapar Sunday, Bernard Francis, Daniel Bulus, Solomon Dung, da kuma wani Yakubu John.

Ragowar wadanda ake zargi sun hada da; Stephen Ishaku, Yohanna Marshal, da Dakwak Sunday.

Muleng Alex tace wadanda ake tuhuma a gaban kotu sun auka wa matafiyan da miyagun makamai, tace Solomon Dung yaro ne da bai cika shekara 18 ba.

Lauyar ta roki Alkali ya tsare Dung a sashen taske kananan yara a gidan gyaran hali na Jos. Alex tace hukuncin wanda ya aikata wannan laifin shi ne kisan-kai.

Jerin wadanda aka hallaka

Jami’an tsaro suna zargin wadannan mutane da aka kai kotu da hannu a mutuwar Sule Alhaji Bechi, Mallam Ahmadu, Sidda Abubakar, da Abdulkarim Mumini.

Haka zalika ana zarginsu da hannu a kisan Suleiman Hassan, Salisu Haliu, Mohammed Nura, Bello Ori, Abdulkarim Snusi, Yakubu Malam Bello da wasu mutum 16.

Rahoton yace Alkali mai shari’a, Arum Ashom, ya dage karar har zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, 2021.

Yadda abin ya auku

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar kwanaki, an kashe wadannan Bayin Allh ne a hanyar dawowarsu daga zikiri a gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Matafiyan sun ziyarci garin Bauchi ne domin yi wa al’umma addu’o’i na musamman yayin da aka shiga sabuwar shekarar hijira ta addinin musulunci na 1443.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN