Duba abin da ya kamata ku sani kan kasuwar dabbobi mafi girma a arewacin Najeriya

 

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kasuwancin dabbobi na daga cikin mafi albarka da kawo riba a yanin arewa maso gabashin Najeriya, inda mutane da gwamnatoci ke samun miliyoyin naira a kullum.

A jihar Adamawa da ke arewa maso gabas, babbar kasuwar dabbobi ta Mubi na daga cikin uku mafiya girma inda masu saye da sayar wa ke zuwa daga dukkan sassan kasar da Kamaru har ma da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka.

Makiyaya na shafe kusan mako daya daga kasashen da aka ambata inda suke kawo dabbobinsu kasuwar dabobi ta Mubi, wajen da ya zama cibiyar kasuwanci a karamar hukumar Yola ta kudu.

Salihu Adamu na BBC ya ziyarci kasuwar kuma ya duba tasirin tattalin arziki a can.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE