An fara bikin lasar gishiri na Kursale a Nijar


A Jamhuriyar Nijar, shirye shirye sun kankama don buɗe bikin lasar gishiri na KURSALE, ta masu kiwon dabbobi.

Yanzu Haka dai garin Ingal ya cika ya tunbatsa da baƙin da suka fito daga sassa daban-daban na Jamhuriyar Nijar da na sauran ƙasashe maƙwabta domin halartar wannan biki.

Bikin na shekara-shekara, muhimmin al'amari ne da ke jan hankulan ɗumbin jama'a musamman masu ruwa da tsaki kan harkar dabbobi.

A duk lokacin damina ake gudanar da wannan biki a kasar ta Nijar.

Dubban garken dabbobine ke hawa kan wuraren kiwon arewacin Ingal, inda suke cin ciyawa mai gishiri dake kara musu lafiya.

Ga masu gudanar da wannan biki a wajensu sallah ce ta musamman makiyaya.

Yawanci buzaye da fulani da ke kiwon manyan dabbobi kamar Rakumi da shanu kai har ma da sauran dabbobi ne ke hadu domin gudanar da wannan biki.

Malam Abubakar Yakubu Ayama, mazauni ne a garin Ingal inda ake gudanar da wannan biki, ya kuma shaida wa BBC cewa, yawanci idan damuna ta fadi sosai ruwa kan taru a gurbi-gurbi, kuma kasar garin ko yankin tana da kanwa da yawa a cikinta dama gishiri.

Ya ce," To Wannan ruwa da ya taru sai ya hade da kasar yakasance akwai dandanon gishiri, to shi ne ake akawo dabbobi domin su zo su sha don yana kara musu lafiya".

Ya ce shi wannan ruwa kamar shi ne sinadarin bitamin na dabbobin.

Ana dai shafe kwana uku ana gudanar wannan biki na lasar gishiri.

Kabilu daban-daban na kasar ne ke halartar wannan biki, kuma su kan tattauna tare da bayar da shawarwari a kan wani abu da ya shige musu duhu.

A kan yi kade-kade da raye-raye a wajen wannan biki, ani lokaci ma har a kan hada da bikin aure a yayin bikin lasar gishirin.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN