Yan Taliban sun kashe wani Gwamna, sun fara dukan jama'a har da kisan yan wasu kabilu (Hotuna)


Ana ci gaba da samun shaidar irin yadda Taliban ke aiwatar da manufofinsu ta hanyar dukan jama'a da cin zarafinsu a fili da rana tsaka, lamari da ke tabbatar da cewa har ila yau da sunan Jihadi an sake komawa gidan jiya shekara 20 bayan kokarin kawo ci gaba a kasar Afghanistan. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Shaidun da ake samu a yanzu, wanda ya hada da faya fayin bidiyon yadda yan Taliban ke dukan mutane ba gaira balle dalili kawai domin suna rike da tutar kasar Afghanistan. Wannan ya faru fiye da dozin goma a birnin Kabul kawai.

Kazalika kungiyar Amnesty international ta yi zargi a wani rahotu cewa, mayakan Taliban sun kashe mutum tara yan kabilar Hazara bayan sun karbe ragamar mulkin gundumar Ghazni wata da ta gabata.

Yan Taliban sun harbe mutum shida da bindiga har Lahira, yayin da suka azabtar da mutum uku har suka mutu. Kazalika yan Taliban sun shake wani ta hanyar yin amfani da rawaninsa yayin da wasu daga cikinsu suka yanke jijiyoyin damtsen hannunsa kiri kiri a wani nau'in azaba.

Wannan ya faru ne tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan Yuli 2021 a kauyen Mundarakht da ke Gundumar Malistan.

Wani bidiyo mai tayar da hankali da ke zagayawa a shafukan intanet, ya nuna yadda yan Taliban suka daure idanun shugaban lardin Badghis, Janar Haji Mullah Achakzai, suka sa ya gurfana a kasa, kuma yan Taliban suka yi masa ruwan harsasai da bindigogi a kusa da Birnin Herat.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari