Raddi ga Sani Dododo: Kai ne Limamin rashin Adalci a jam'iyar APC jihar Kebbi, har ka gudu ka bar ladar ka


Yan kwanakin bayan Sani Dododo ya zargi jamiyar APC a jihar Kebbi da aikata ba daidai ba a zaben shugabannin jam'iyar a fadin jihar. Yana mai nuni da cewa an yi "Dauki dora" marmakin zaben shugabannin. An gano wadannan kalamai da aka alakanta da Dododo a shafukan sada zumunta kuma bai karyatasu ba. 

Sakamakon haka masani, Mawallafi kuma tsohon jami'in tsaro da ayyukan sirri na cikin gida (DSS) Malam Isyaku Garba, ya kalubalanci Dododo bisa zargin neman tayar da hankalin jama'a mabiya jam'iyar APC a jihar Kebbi domin su yi bore ga jam'iya ta hanyar kirkiro kalamai da ya saba amfani da su matukar bai sami abin da yake so ba wanda a nawa fahimta shi yake nufi da kalmar "Adalci".

Da farko ni Isyaku Garba na kalubalanci Sani Dododo ya yi wa jama'a bayani me yake nufi da kalmar "Adalci".


Kantama kantaman rashin Adalci da Sani Dododo ya yi 

1 Ranar 11 ga watan Afrilu 2019, a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi, Sani Dododo ya shiga zancen da bai shafe shi ba. 

(a) Zance ne da ya shafi kungiyar masu sayar da waya da gyaran waya na jihar Kebbi.

(b) Kawo yanzu bamu da tabbacin cewa Dododo Yana sayar da waya ko gyaranta.

(c) Zancen na ofishin Sakataren Gwamnatin ne Babale Umar kuma a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin ne aka yi zancen.

(e) Babu hadi tsakanin ofishin da yake shugabanta a wancan lokaci State Emergency Management Agency SEMA da matsalolin da suka shafi kungiyoyi musamman na masana da kwararru.

(f) Shigar Sani Dododo cikin lamarin ya kara kawo rarraba, gaba, rashin mutunci da rashin ci gaba tsakanin yan kungiyar.

(g) Sakamakon kalamansa an kasa samun daidaito lamari da a karon farko har magana ta kai Kotu kuma har yau shari'ar bata kare ba bisa alkalumma da muka samu.

Da irin wannan hali har Sani Dododo yana da muru'a da zai yi zancen cewa APC ta yi rashin Adalci a jihar Kebbi?


Latsa nan ka karanta irin cin mutunci da Sani Dododo ya yi wa Isyaku Garba a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin ranar 11 ga watan Afrilu 2019

2. Ranar 14 ga watan Oktoba 2019, an gudanar da kwatan kwacin irin wannan zabe a jihar Kebbi, har mutanen karamar hukumar Sakaba suka zo garin Birnin kebbi suka yi zanga zanga. Sani Dododo yana rike da mukamin Kakakin jam'iyar APC na jihar Kebbi.  Wane martani ya bayar a lokacin game da korafe korafen da jama'a suka yi? 

Idan ya manta za mu tuna masa.

Duba wannan labari wanda ya faru lokacin da Sani Dododo yake rike da mukamin Kakakin jam'iyar 
APC na jihar Kebbi a 2019. 


Wane martani Dododo ya bayar ? Sai a yanzu ake rashin Adalci a jam'iyar APC a jihar Kebbi bayan ya tsere daga kan kujera da jam'iyar APC ta yi masa alfarmar zama a kanta tun 2015?

3. A watan Agusta 2019. An gudanar da zaben fitar da Gwani na Yan Majalisar Wakilai na tarayya a jihar Kebbi, lamari da ya kai ga karbe kujerar Hon Abdullahi Muslim da abin da ake zargin an aikata ba daidai ba ta hanyar amfani da Exco na jam'iyar APC, a matsayinsa na Kakakin jam'iyar APC na jihar Kebbi ya manta da martani da ya yi ne? Za mu tuna masa daidai lokacin da ya dace.

(a) An gudanar da zaben fidda gwani na mukamin Gwamnan jihar Kebbi ranar 29/9/2021, an yi korafe korafen rashin Adalci, me Dododo ya ce?

(b) An gudanar da zaben fidda gwani na kujerar Sanatoci da Yan Majalisar tarayya a jihar Kebbi ranar 2/10/2019, an yi korafe korafen rashin Adalci, me Dododo ya ce?

(c) An gudanar da zaben fitar da gwani na kujerun Yan Majalisar dokoki na jihar Kebbi ranar 4/10/2021, me Dododo ya ce?.

4 A baya bayan nan, an sami wani dan rashin fahimta a cikin jam'iyar APC a jihar Kebbi, lamari da ya kai ga dakatar da wasu shugabannin jam'iyar a fadin jihar Kebbi. Wadanda dakatarwar ta shafa basu dinga yin babatu kan jam'iyar APC ba. Dododo ya fi su ne?  Mi ya sa ya yi murabus kafin Kwamiti ya kammala bincike kuma kowa ya fuskanci hukunci?.

{a) Dododo ya fi shugaban jam'iya da Sakataren kudi na jam'iyar ne? da jam'iya ta dauki matakin Kuma suka yi hakuri suka ci gaba da zama a jam'iyar kuma suna yi mata da'a? 

(b) Takarda ce ta nada shi a kan mukaminsa, ita ya kamata ta saukar da shi ba wai ya zauna a gida ya nada bidiyo a waya ya ce ya sauka daga mukaminsa ba.

(c) Ya kamata jam'iyar APC ta tilasta Dododo ya yi mata bayani a rubuce dalilin da ya sa ya sauka daga mukaminka. Kuma ta bincike shi matuka idan bata gansu da bayaninsa ba. Kazalika, Muna kira ga jamiyar APC na jihar Kebbi, ta binciki yadda Dododo ya yi amfani da kujerarsa wajen hulda ja yan jam'iya da jama'a a jihar Kebbi daga 2015 zuwa yanzu.

Ko kalaman Sani Dododo cin mutunci Gwamna ne?

A karon farko, mun karanta a shafukan sada zumunta wai Sani Dododo yake shawartar Gwamna a shafukan sada zumunta.  Wannan a ra'ayi na, ya nuna lallai akwai lauje a cikin nadi. Kuma alama ce da ke saukar da ayar tambaya. Tambayar kuwa it ce,... Sani Dododo masoyin Gwamna ne? Masoyin jihar Kebbi ne? Masoyin jam'iyar APC na jihar Kebbi da ta raya shi da mukamin Kakakinta ne? Kuma haka kawai ya gudu ya bar kujerar alfarma da ta yi mashi ?. 

Jam'iyar APC a jihar Kebbi tana nan daram ba za ta watse ba

A kalaman da aka danganta su da Sani Dododo a shafukan sada zumunta, ya ce rashin Adalci da aka yi ya sa jam'iyar APC ta kama hanyar watsewa. Sai dai wani bincike da na gudanar, ya tabbatar da cewa hasashen iska ne kawai Dododo ya yi. Amma 'ya'yan jam'iya suna nan kan su hade a waje daya, kuma har yanzu suna biyayya ga jmiyar APC na jihar Kebbi da uwar jam'iya ta kasa. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN