Yadda maigida ya yi wa matarsa mugun duka ya zaneta da belt, duba abin da ya faru


Wani magidanci mai shekara 34, Timothy Shikaan, dan asalin jihar Benue, amma yake da zama a Temple Clinic da ke garin Asaba jihar Delta, ya yi wa matarsa mai suna Mrs Shikaan dukan tsiya a gidansu.

Sakamakon yawan dukan matarsa, an yi kararsa wajen wani dan karadin kare hakkin dan adam Harrison Gwamnishu, kuma Darakta Janar, DG na Behind Bars Human Rights Foundation, nan take ya kai wa mijin matar ziyara.


A cikin gidan, an gan yadda matar ta sha duka a wajen mijinta har shafin zaneta da Belt da mijin ya yi mata ya bayyana a hannu da bayanta.

An mika mijin wajen DPO na yansanda a garin Asaba, kuma yansanda sun garkame shi ana gudanar da bincike. 

 Kalli bidiyo a kasa:


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN